Da Dumi Dumi: Kasar Jamus zata taimakawa da Palasdinawa agajin Yuro Miliyan 40.

Jamus ta yi kira da a tsagaita wuta tare da ba da karin taimako.

A Yau ne Firaminista Heiko Maas na kasar Jamus yayi kira da a tsagaita wuta a yakin da ake tsakanin dakarun Palasdinawa da Sojojin Yahudawan Isra’ila a Gaza

Infa yae “A yau, zan shiga neman samar da kayan agaji mafi kyau a Gaza,”

Haka kuma Firaminista Heiko Maas, ya yi alkawarin kashe yuro miliyan 40 ($ 48.86m) don kai kayan agaji ga fararen hula a Gaza.

Har yanzu dai anata gumurzu tsakanin dakarun Palasdinawa da kuma Sojojin Yahudawan Isra’ila, inda ita Isra’ila taki amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Shima shugaban kasar Amurka Mr. Joe Beiden ya nemi Isra’ila ta tsagaita wuta, amma ta yi kunnen uwar shegu dashi.

Tuni dai kasashen Musulmai irin su Turkiya suka fara shirye shiryen kaiwa kasar Isra’ila harin ramuwar gayya akan ta’addancin da take aikatawa akan Palasdinawan, abin jira a gani dai bai wuce yadda za a magance fadan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *