Kasashen Ketare

Da Dumi Dumi: Ministoci uku na Ukraine sun mutu a yayin da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a kusa da kindergarten a Kyiv

Spread the love

Akalla mutane 18 da suka hada da kananan yara biyu ne suka mutu bayan da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hadari kusa da wata makarantar renon yara a Kyiv, babban birnin Ukraine.

Denis Monastyrsky, ministan cikin gida na Ukraine, da wasu ministoci uku su ma sun mutu a hadarin da ya faru a ranar Laraba.

Oleksiy Kuleba, shugaban hukumar soji ta yankin Kyiv, ya ce bala’in da ya faru a Brovary ya yi sanadin jikkatar mutane 29 tare da kashe 18.

Ya kara da cewa gobara ta tashi ne bayan da jirgin mai saukar ungulu ya fado.

Babu bayanin abin da ka iya haifar da hatsarin.

A lokacin da abin ya faru, akwai yara da ma’aikata a makarantar renon yara. A halin yanzu an kwashe kowa da kowa.

A cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan sandan Ihor Klymenko ya fitar, ya ce akalla tara daga cikin wadanda abin ya shafa na cikin jirgin mai saukar ungulu wanda na hukumar ba da agajin gaggawa ta Ukraine ce.

Ya kara da cewa wasu mutane 22 suna kwance a asibiti, ciki har da yara 10.

Jami’an agajin gaggawa, ‘yan sanda, da ma’aikatan kashe gobara na kai dauki a wurin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button