Kasashen Ketare

Daular Larabawa Ta Aiko Da Tallafin Kayan Abinci Zuwa Najeriya.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Firayim Ministan Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, ya umarci jamiā€™ai a kasarsa da su tura kayan agaji na gaggawa da kayan abinci zuwa Najeriya.

Ofishin jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa a Najeriya shine ya sanar da hakan a wani sakon Twitter.

Dangane da tallafin, Maktoum ya bayyana cewa, wannan na cikin yunkurin da kasar take na tallafawa Najeriya a kokarin da take na yaki da cutar Coronavirus.

Kayan sun hada da, Tan bakawai na kayayyakin kiwan lafiya, da kuma Tan biyar na kayan Abinci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button