Gwamnatin Faransa ba ta goyon bayan batanci ba ga Musulunci – in ji shugaban Faransa Macron.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a wata tattaunawa da gidan talabijen na Al Jazzira, ya bayyana cewa ko kadan manufar sa ba ita ce ta haifar da bacin rai ko janyo rikici tsakanin Faransa da kasashen musulmai aminan Faransa ba.

Shugaban ya bayyana cewa manufar sa a matsayin Shugaban kasa, nauyi ya hau kan sa don kare muradun kasar da kuma baiwa kowa ‘yanci fadar albarkacin bakin sa, ko kadan gwamnati ba ta da hannu a batun zane-zane jaridar Charlie Hebdo mai zaman kan ta kamar sauran kaffofin yada labaran Faransa.

Shugaban ya jaddada aniyar hukumomin kasar na mutunta addini musulunci.

Faransa za ta tura jakadan ta Turkiya a yau Lahadi, wanda zai kuma samun tattaunawa da hukumomin kasar kamar dai yadda ministan harakokin wajen kasar Jean Yves Ledrian ya sanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.