Juyin Mulki: Sojojin Kasar Mali Sun Kama Shugaban Kasar Ta Karfi Da Yaji.

Yanzu yanzu sojojin kasar Mali sun kama shugaban kasar Mali Bubacar kaeita da firaministan kasar ta Mali.

Kasar faransa da kungiyar ECOWAS sunyi Allah wadai da yunkurin da sojojin kasar ta Mali sukeyi Na mayar da hannun agogo baya a kasar ta Mali.

Idan baku manta ba an dade ana rikicin siyasa a Kasar tsakanin shugaban kasar da ‘yan adawar Kasar.

Ko a kwanakin baya ma sai da Kungiyar ECOWAS ta tura tsohon shugaban kasar Najeriya Dr. Goodluck Jonathan domin ya sasanta rikicin, amma hakan bai yiwu ba.

Haka zalika shuwagabannin Kasashen Afika ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sunje da nufin shiga tsakani, Amma aka kasa samun jituwa.

Yanzu Dai abin jira agani bai wuce matakin da Sojojin zasu dauka akan shugaban ba.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published.