
A kasar Bosnia, wani tsoho ne mai kimanin shekaru 72 ne ya ciri tuta a binin masoya, yayin da ya kirkirirar wa sahibarsa gida sukutum, gida ba irin kowanne gida amma shi wannan gida, gidane mai juyawa duk don ganin burge wannan tsaleliyar matarsa da ta kasance tana takura masa akan burin ta nason ganin kwakwaf.
Tsohon mai suna, Vojin Kusic ya ce tsabar gane-gane da matarsa take dashi ne dalilin da yasa yake yawan sauya fasalin gidansu domin ta rika samu tana ba wa idanunta abinci ta hanyar ganin irin abin da ke faruwa a waje, bugu da kari wannan dalilin ne yasa yanzu tsoho ya zama mai kirkira, karfi da yaji.
Dattijon ya kara da cewa, ko yaya matar tasa ta samu dama, kallo take tsayawa ta yi, wani zubin ma harda dalalar da yawu.

Wannan dalilin gamida yawan tereren da take yawan yi masa ya sa shi tunanin yadda zai yi ya mayar da gidan nasu ta yadda zai rika juyawa ta kowace kusurwa, domin matar ta samu ta rika kashe kwarkwatar idanunta.
“Gajiya na yi da yawan gunaguninta a-kai-a-kan cewa a sauya fasalin gidanmu, shi ne na ce ‘To bari zan gina miki gidan da zai riga juyawa saboda ki rika juya shi yadda kika ga dama’,” inji shi.
Kawo ya zuwa yanzu dai ya kirkiro gamida da gina mata wani gida wanda yake juyawa da ilahirin gidan kamar fanka, Wannan juyawa da gidan yake yi, shi zai sa ta ga duk abin da take son gani a waje, daga duk inda take a cikin gidan.

Da yake bayanin yadda gidan yake, Mista Kusic ya ce:
“Idan aka rage gudunsa zuwa karshe, gidan zai dauki awa 24 yana tafiya har ya juyo zuwa daidai inda ya fara tafiya.
“Idan aka kure gudunsa kuma, a cikin dakika 22 gidan zai iya juyawa zuwa daidai inda ya fara tafiya.”

Yanzu haka dai a kasar, mutane ne ke tayin tururuwar zuwa ganin gidan na Mista Kusic daya gina wa matar tasa , kuma yanzu haka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa shi ba injiniya ba ne, kuma ba shi da wata kwarewa a fannin kirkira.

Tsohon ya ce, hasali ma bai halarci wata makarantar ku-zo-ku-gani ba saboda gidansu talakawa ne, shi kuma a matsayinsa na talaka dole ya nemo yadda zai rika yi wa kansa abin da yake bukata.
Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru