Kisan Ƙare Dangi: Wani mutumi ya kashe matarsa da ’ya’yansa biyar da surukarsa.

Binciken da ‘yan sandan suka yi ya nuna cewa ya aikata kisan kai ne bayan da matarsa ta nemi saki.
Michael Haight, mai shekaru 42, ya halaka dukan iyalinsa, bayan ya kashe matarsa, surukarsa da ‘ya’yansa biyar kafin ya kashe kansa a Utah, Amurka.
Binciken da ‘yan sandan suka yi ya nuna cewa ya aikata kisan kai ne bayan da matarsa ta nemi saki.
An gano gawarwakin dangin da aka kashe a wani gida da ke birnin Enoch a ranar Laraba bayan da aka ce Misis Haight ta rasa wani alƙawari da ta tsara ba tare da bayar da wani bayani ba. Rahoton ya sa aka duba lafiyarta a gidanta.
Wadanda Mr Haight ya kashe sun hada da matarsa Tausha ‘yar shekara 40, surukarsa Gail Earl mai shekaru 78 da ‘ya’ya biyar da ba a bayyana sunayensu ba saboda yara kanana ne. Yaran da aka kashe sun hada da ‘yan mata uku masu shekaru 17, 12 da 7, da maza biyu masu shekaru 7 da 4.
Rob Dotson, manajan birnin Enoch ya bayyana cewa duk wadanda abin ya shafa sun mutu sakamakon harbin bindiga.
Jami’an tsaro sun ce Misis Haight ta bukaci a raba aurenta ne a ranar 21 ga watan Disamba, kwanaki kafin mijinta ya fara jin haushi.