Kasashen Ketare

Ajali: Wata Daliba da take karantar fannin shari’a ‘yar shekara 23 ta mutu bayan ta sha Alewar da ta siya ta yanar gizo.

Spread the love

Wata daliba mai suna Damilola Olakanmi ‘yar shekara 23 da ke karatu a kasar Burtaniya, ta mutu bayan ta sha kayan zaki da ta siya ta yanar gizo.

Olakanmi, wacce ke zaune a Ilford da ke gabashin Landan tare da mahaifiyarta, an ruwaito cewa ta sayi ‘gummies’ ta hanyar manhajar aika sako kuma an kai su gidanta inda ta yi rashin lafiya a ranar Talatar da ta gabata.

A cewar Mirror UK, Olakanmi ta shanye ‘sweets’ din tare da kawarta mai shekaru 21, kuma nan da nan dukkansu sun kamu da rashin lafiya bayan kowannensu ya sha daya daga cikin ‘zaƙi’. Yayin da kawarta ta tsira, ita kuma ta rasu.

An ruwaito Olakanmi ita ce diya tilo ga mahaifiyarta.

A halin yanzu, an kama wani wanda ake zargi, Leon Brown, mai shekaru 37, kuma an tuhume shi da mallaka da samar da nau’in cannabinoid na Class B, da damuwa a cikin samar da cannabinoid na roba, da kuma mallaka da samar da wani abu mai hadari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button