Na kaɗu da mutuwar ɗalibai a Jamhuriyar Nijar. -Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa bisa ga iftila’in gobara wanda yayi sanadiyar mutuwar ɗalibai aƙalla 20 a garin Yemen dake Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Buhari ya bayyana iftila’in gobarar da yayi sanadiyar mutuwar yara waɗanda basu wuce shekaru uku-zuwa-huɗu ba a matsayin al’amari mai mutuƙar taɓa zuciya; ya bayyana hakan ne a wani saƙon ta’aziyya na musamman da ya aikewa takwaransa na Nijar, Mohammed Bazoum ranar Asabar.

Amadadin gwambanti da ɗaukacin al’ummar Nigeria muna miƙa sakon ta’aziyya ga maƙwabtan mu Nijar bisa ga wannan mummunan iftila’i daya faru da su؛

A ƙarshe yayi addu’a ga waɗanda al’amarin ya shafa, tare da fatan samun sauƙi ga ɗaliban da suka tsira da munanan raunuka.
Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa.

Rahoto; Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *