
Wani ɗan Najeriya wanda daɗi yayi wa katutu ya ɗauko dala babu gambo.
Domin kuwa yanzu zancen da akeyi, mutumin mai suna Kunle Adeyanju ya soma wata doguwar tafiya, tafiya salon gudu-gamai-ƙareka tun daga can Ingila zuwa nan Najeriya, inda yake fatan tsaida tafiyar tasa a birnin Legas.
Adeyanju ya bayyana hakan ne a wani wallafaffen rubutu daya wallafa a shafin sa na Twitter, inda ya bayyana cewa tafiyar zata soma ne daga wannan talatar.

Yace zaiyi, somin taɓi ne daga Landan zuwa Borges dake ƙasar Faransa, sannan ragowar ya ƙarƙare ta a cikin kwana 25.
Mutumin ya zayyana cewa, yana sa ran keta ƙasashe da dama, cikin su kuwa sun haɗa da Andalus (Spain), Senegal, Ghana da kuma Togo.
A cewar sa:
“A yau na soma tafiyar nan tasa kai daga London zuwa Legas a 19 ga watan Afrilu. Tafiyar ina sa ran ta ɗauke ni kwanaki 25, kuma zanyi tafiya mai nisan kimanin kilomita dubu goma sha biyu (12,000km/h)”.Ya wallafa.

Ko wani ko irin fata kuke masa?
Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru