Kasashen Ketare

‘Yan wasan Morocco da jami’an hukumar wasanni na ƙasar sun samu lambobin yabo na sarauta saboda bajintar da sukai a gasar cin kofin duniya

Spread the love

An bayar da lambobin yabo na sarauta ga ‘yan wasan da kuma jami’an kungiyar kwallon kafa ta kasar Morocco sakamakon rawar da suka taka a gasar cin kofin duniya ta FIFA na Qatar 2022.

Kungiyar Atlas Lions ta kafa tarihi a gasar cin kofin da aka yi a Qatar inda ta zama tawaga ta farko a Afirka da ta kai wasan kusa da na karshe a gasar duniya.

A kan hanyarsu ta zuwa zagayen hudun karshe, sun baiwa wasu manyan kungiyoyin Turai mamaki, da suka hada da Belgium, Spain da Portugal, sannan kuma ba su dandana kudarsu a matakin rukuni ba.

Guguwarsu mai ban mamaki ta kare ne bayan da suka sha kashi a hannun Faransa da ci 2-0 a wasan kusa da na karshe, kuma sun yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Croatia a wasan na uku.

A cewar kamfanin dillancin labaran kasar Moroko MAP EXPRESS, bayan isowar tawagar daga Qatar a ranar Talata, Sarki Mohammed VI tare da ‘ya’yansa, Yarima Moulay El Hassan da kuma Yarima Moulay Rachid ne suka karbi bakuncin tawagar.

‘Yan wasan sun zo ne da iyayensu mata, da kuma masu horar da ‘yan wasa tare da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Fawzi Lakjaa a taron da aka gudanar a Rabat.

A yayin liyafar, Sarki Mohammed na shida ya yiwa shugaban hukumar da koci Walid Regragui ado da lambar yabo (Rank Of Commander).

Sarkin ya kuma yi wa duk tawagar Atlas Lions 26 ado da Order of the Throne (Rank Of Officer).

Har ila yau, ya ba da umarnin a ba da lambobin yabo na sarauta ga dukkan ma’aikatan fasaha da likitoci na tawagar kasar, don jin dadin aikin da suke yi a Qatar.

Bayan haka, Sarkin tare da ‘ya’yansa maza sun dauki hoton tunawa da ‘yan wasan kasar da iyayensu mata.

Kafin su gana da sarkin, ‘yan wasan sun samu tarba daga isowar dubban magoya bayansu da suka yi jerin gwano domin hango jaruman nasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button