Tsaro
Kashe Jama’a A Kaduna: Rahama Sadau Ta Bara..
Fitacciyar Jarumar fina finan Hausa ta kannywood Rahama Sadau Ta tofa albarkacin bakinta akan kashe kashen jama’a da ake yi a Kudancin Kaduna.
Jarumar ta roki gwamnatin Tarayya da na Jihohi da su taimaka su kawo karshen al’amari.
Rahama Sadau tace “Na tsaya ina kalubalantar kashe-kashe a Kudancin Kaduna. Ina kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su tabbatar da yanayi mai kyau ga dukkan yan Najeriya. Don Allah! 🙏🏻”.
Rahama Sadau Ta fadi hakan ne a shafinta na Twitter, Kuma tuni mabiyanta sukatita yin tsokaci akan kalamin nata, mafi akasari suna nuna yabawarsu ne agareta.