Kungiyoyi
Kashe-kashe Na Bata Canjin Da Buhari Ke Son Kawowa, Inji Kungiyar Matasan Najeriya.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Wata kungiyar matasan Najeriya me suna, NYCN ta koka kan yawan kashe-kashe wanda tace suna bata Canjin da shugaban kasar ke son kawowa Najeriya.
Kungiyar ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya mayar da hankali wajan magance matsalar satar Mutane da ta Boko Haram.
Kungiyar ta aikewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da budaddiyar Wasika ta hannun shugabanta, Solomon Adodo,kamar yanda Mun samo muku, inda tace zata ci gaba da goyawa tsare-tsaren shugaban kasar na ci gaban Najeriya baya.