Labarai

Kashe-kashen da ake a mulkin Buhari ya ninka na mulkin Jonathan~Sheikh Gumi

Spread the love

A Cikin wani sabon bidiyonsa Sheikh Gumi ya kaiwa Buhari hari, ya roke shi da ya yi murabus nan take Daya daga cikin manyan malamai musulman Nageriya Sheikh Dr, Ahmad Abubakar Gumi ya fito karara ya kaiwa Shugaba Buhari hari a kan kashe-kashen da ake yi da kuma kashe manoman shinkafa 43 a garin Zabarmari na jihar Borno.

Shuhun malamin Ya ce kashe-kashen da ake yi a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari a yanzu sun ninka na gwamnatin da ta gabata, kuma ya umarci Shugaba Buhari ya yi murabus nan take.


Shehin ya kuma kara da cewa an kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba saboda gazawar gwamnatin mai ci. Shahararren mai wa’azin nan kuma masanin shari’ar Islama a Babban Masallacin Kaduna yayi wadannan bayanan ne yayin daya ke gabatar wa’azin nasa kwanan nan. Sheikh Ahmad Abubakar ya kasance tsohon jami’in soja tare da mukamin kaftin kuma tsohon likita ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button