Kashe Mutane Da Yawa Yayin Rikici Da ‘Yan Bindiga A Katsina.
Rikici tsakanin sanannun sansanonin ‘yan fashi guda biyu ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata.
Kungiyoyin ‘yan fashi biyu sun yi arangama a kauyen Illela na karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina, inda suka bar da yawa daga cikinsu suka mutu wasu da yawa kuma suka jikkata.
Rikicin, tsakanin sansanin Mani Sarki da Dankarami da ke marawa sansanin Abu Rada baya, ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa Sarki, wanda yanzu ya tuba, ya karbi afuwar gwamnati kuma ana ganin sa a matsayin saniyar ware daga wasu sansanoni da ke dazuzzuka.
An tattaro cewa amincewa da afuwar ya tilasta Sarki komawa kauyen Illela don fara sabuwar rayuwa, amma wasu daga cikin yaransa sun ki tafiya tare da shi.
Wata majiya ta ce: Wasu ‘yan bindiga karkashin jagorancin wani Dan Da daga kungiyar Alhaji Dankarami sun kai wani hari a yankin Illela, amma sai sauran ‘yan kungiyar suka fatattake su, lamarin da ya sa suka yi watsi da makamansu, ciki har da bindigar kakkabo jiragen sama wadanda duk aka tafi da su. ta maharan a matsayin ganima. Hakan ya fusata su kuma basu manta da shi ba.
Abu na biyu, kane ga Sarki Mani, a wani lokacin ya saci matar daya daga cikin mutanen daga bangaren Dangwate kuma an biya shi kudin fansa N500,000 kafin ya sake ta.
Daga Aliyu Adamu Tsiga