Kasuwanci

Ba zan damu da sayen man fetur a kan Naira 300 ba, Naira 300 kan kowace lita ai babu tsada – Ministan Mai

Spread the love

Timipre Sylva, karamin ministan albarkatun man fetur, ya ce ba zai damu da sayen man fetur a kan Naira 300 ba.

Sylva ya fadi haka ne a ranar Litinin a jerin lissafin gwamnati mai taken ‘PMB Administration scorecard 2015-2023’.

An shirya taron ne domin nuna irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015.

Sylva, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa, ya ce wasu kasashe suna sayar da kayayyakinsu a farashi mai yawa fiye da na Najeriya, don haka Naira 300 kan kowace lita babu tsada.

“A gaskiya, idan ka tambaye ni zan ce ba zan ji dadi ba (siyan man fetur a kan Naira 300) da sanin hakikanin halin da ake ciki. Amma idan ka kwatanta Najeriya da sauran kasashe, to kai ma za ka gane N300 din be yi tsada.” Inji shi.

“Yawancinku suna tafiya Burtaniya da Amurka. Nawa kuke siyan man fetur? Ko a kasar Saudiyya da kasashen Larabawa da suke hako danyen man fetur, idan kuka canza Naira, za ku ga ba mu yi mugun aiki ba.”

Hakazalika, Sylva ya ce, idan har kasuwa ce take ƙayyade kudin man fetur, masu zuba jari ba za su ci gaba da yin watsi da saka hannun jari a bangaren mai ba.

Ya kara da cewa masu zuba jari ba za su zo kasar nan a karkashin tsarin tallafin ba, amma ya ce za su yarda su sanya kudadensu a fannin idan kasuwa ta samu ƴancinta.

“A karkashin tsarin tallafi, wa zai saka jari? Idan kun gina matatar mai, ta yaya matatar ku za ta samu riba a karkashin tsarin tallafi? Amma idan kuna da yanayin kasuwa, za ku ga cewa masu zuba jari da yawa za su zo,” inji shi.

“Kuma zamu sami ƙarin yawan matatun mai da muke da su, wannan matsalar samun albarkatun man fetur za ta zama tarihi.”

Sylva ya kara nanata cewa tallafin man fetur ba ya dauwama kuma baya samun riba.

“Gudanar da yanayin samar da kayayyaki a karkashin wannan tsarin tallafin ba abu ne mai sauki ba. Dole ne dukkanmu mu yarda [cewa] ana kona makudan kudade akan motocin mu. Amma ko ta yaya sai mun nemi kudi domin a jika kasar nan,” inji shi.

Sylva ya kuma kara da cewa, ya kamata a jinjina wa gwamnatin tarayya kan inganta tsaro a yankin Neja Delta, wanda ya taimaka wajen kara yawan man fetur.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta karfafa sa ido kan yadda ake samar da kayayyaki da kuma rarraba kayan aiki, ta yadda za a inganta tsaro a wuraren aiki.

Dangane da nasarorin da ma’aikatar ta samu, Sylva ya ce ta sami damar zartar da dokoki masu mahimmanci kamar dokar ruwa mai zurfi da na cikin gida da kuma dokar masana’antar man fetur (PIA), ya kara da cewa yana kuma inganta shigar da ‘yan asalin kasar ta hanyar samar da danyen mai da saukin lasisin yarda.

Ya ce an samu raguwar farashin danyen man da aka yi hasashen kashi 5 cikin 100 kuma ya zarce a tsawon lokacin.

Bugu da kari, ministan ya ce, kananzir ba ta cikin hannun gwamnatin tarayya kai tsaye, tun da yanzu an kayyade farashin, inda ya yarda cewa, ya ci gaba da zama man fetur ga marasa galihu.

Sylva ya kuma jera shirin sayar da iskar gas – wanda ya ce yana mataki na karshe na bayar da maki ga wadanda za su yi nasara – a matsayin daya daga cikin nasarorin da gwamnatin yanzu ta samu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button