Kasuwanci

Buhari Da Pantami Sun Yi Farin Ciki: Kamfanin Microsoft Zai Horar Da ‘Yan Nijeriya Miliyan Biyar.

Spread the love

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kamfanin Microsoft Corporation Brad Smith tare da Hon. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital Isa Ali Ibrahim Pantami yayin taron sa tare da Shugaban Kamfanin Microsoft a Gidan Gwamnati a ranar 1 ga Afrilu 2022.

Katafaren kamfanin kere-kere, Microsoft ya ce zai horar da akalla ‘yan Najeriya miliyan biyar nan da shekaru biyu masu zuwa a wani bangare na kokarin taimakawa kasar wajen bunkasa tattalin arzikinta na zamani.

Shugaban Microsoft, Brad Smith, ya bayyana haka a ranar Juma’a lokacin da ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati.

A cewar Smith, mutane 60,000 sun riga sun shiga kwasa-kwasai yayin da wasu 300,000 suka kammala wasu kwasa-kwasan.

Wannan dai na zuwa ne makonni bayan da kamfanin ya kaddamar da cibiyar raya Afirka da ta kai dalar Amurka miliyan 200 da ke Legas.

Shugaba Buhari ya yaba da wannan ci gaban, yana mai cewa kasar na farin cikin maraba da karin ayyuka da saka hannun jari a fasahar zamani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button