Kasuwanci

Dangote ya shirya sabbin ayyuka 300,000 ga ‘yan Najeriya

Spread the love

Babban hamshakin attajiri a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, ya yi hasashen cewa sabon saka hannun jari na biliyoyin Naira a bangaren sukari zai taimaka wajen samar da ayyukan yi kasa da 300,000 a Najeriya.

Sanarwar da Sashen Sadarwa na Kamfanin, ya fitar ta ce, Shugaban rukunin, Dangote ya ce kamfanin na samar da sabbin kudade don fadada ayyukansa a bangaren sukari.

Dangote, wanda ke magana a wajen taron kaddamar da tuta na shekarar 2022/2023 da aka yi a Numan, Adamawa, ya ce damar da za ta samu za ta hada da ayyuka kai tsaye da kuma wanda ba kai tsaye ba.

Ya ce: “Muna zuba jari mai yawa a jihar Adamawa ta hanyar fadada karfin tace sukari na DSR Numan daga 3000tcd zuwa 6000tcd, 9800tcd, zuwa 15,000tcd.

“DSR za ta iya samar da ayyukan yi kusan dubu dari uku, kai tsaye da kuma kaikaice, tare da tasiri mai yawa ga tattalin arzikin kasa.”

Rukunin Dangote shi ne babban ma’aikaci a Najeriya a wajen gwamnati.

An nada Dangote a matsayin shugaban kwamitin samar da ayyukan yi na kasa a shekarar 2010 domin taimakawa gwamnatin tarayya wajen samar da karin ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.

Shugaban na Dangote ya kuma bayyana cewa kamfanin na sa na rubanya kudaden da yake kashewa kan tsare-tsaren CSR a cikin al’ummomin da ke zaune a jihar Adamawa, inda aka gina kadada 32,000 na hadaddiyar sukari.

Da yake jawabi a garin Numan, Ministan Masana’antu, Ciniki, da Zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo, ya bayyana matatar sukari ta Dangote a matsayin babbar mai bayar da gudunmawa wajen ci gaban kokarin gwamnatin tarayya.

Ministan ya kuma yabawa Dangote bisa wannan gagarumin tallafin ta hanyar tsarin sa na daukar nauyin al’umma.

Hakazalika, ana sa ran matatar man Dangote za ta samar da guraben ayyukan yi kimanin 250,000 idan an kammala a shekara mai zuwa.

Tuni Dangote Cement Plc yana daya daga cikin manyan masu samar da ayyukan yi a Afirka a fannin masana’antu.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button