Kasuwanci

Gwamna Ganduje ya fusata ya rusa shugabancin kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano.

Spread the love

Sakamakon rashin shirya sabon zabe bayan karewar wa’adinsu, gwamnan jihar Kano, Dr Umar Abdullahi Ganduje ya rusa shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Kano, KACCIMA, ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan ya fusata kan yadda jami’an zartaswar da aka kora suka yi zaman dirshan, inda ya ba da umarnin tsige su cikin gaggawa.

A cewar wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya sanyawa hannu, ya zama wajibi a dauki matakin ne saboda gazawar shugabannin hukumar na yanzu wajen shirya sabon zabe mai karbuwa tun bayan karewar wa’adinsu. .

Sanarwar ta kara da cewa, tuni Gwamna Ganduje ya amince da kafa kwamitin riko mai mutane tara, karkashin jagorancin wani dan kasuwa mai masana’antu, Alhaji Lawan Sale Garo.

Sharuɗɗan kwamitin, da dai sauransu, sun haɗa da shirya zaɓe cikin watanni shida, tare da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan ayyukan majalisar.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Ambasada Muktari Gashash a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatar kasuwanci, Dr Salim Saleh Muhammad, Alhaji Yakubu Uba, Alhaji Tijjani Usman, Alh. Kabiru Hamisu Kura, Hajiya Aisha, Sulaiman Baffa, Alhaji Bashir Dado da Bauran Gaya.

Da yake jawabinsa shugaban kwamatin, Garo ya nuna jin dadinsa ga gwamnan bisa amincewar da aka basu tare da bada tabbacin cewa kwamitin zai yi bakin kokarinsa wajen cimma burin da aka sanya a gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button