Gwamnati Ta Hana ‘Yan Kasuwa Bude Shagunansu Amma Kuma Ta Kasa Hana Ta’addanci Da Garkuwa Da Mutane A Yankin Birnin Gwari- Inji Wasu ‘Yan Kasuwa A Kaduna.

Daga Sabiu Danmudi Alkanawi.

Da safiyar yau ne ‘yan kasuwa a jihar Kaduna sukayi ido hudu da motocin jami’an tsaro kewaye da shagunansu.

‘Yan kasuwar dai sun kasance suna fito da kayansu waje bakin kasuwa su karkasa saboda kulle kasuwanni da gwamnatin jihar Kaduna tayi tun bayan bullar cutar Korona Bairos.

Sai dai kuma a yau suna fitowa sukayi arba da jami’an tsaron ‘yan sanda da sojoji dauke da makamai kai ka ce zasuje sambisa kamo shekau.

Jami’an tsaron sun hana ‘yan kasuwar kasa kayansu kamar yadda suka saba, sannan sun zagaye kasuwannin yadda ko Aljani bai isa yashiga ba.

Wakilinmu na jihar Kaduna Muktar Onelove ya sami zantawa da wasu daga cikin ‘yan kasuwar, inda suka nuna takaicinsu game da yadda gwamnatin ta hanasu cigaba da kasuwancinsu.

Wani dan Kasuwa da muka sakaya sunansa ya ce “kamata yayi gwamnati ta tura jami’an tsaron yankin Birnin Gwari su yaki ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, gwamnati ta hana ‘yan kasuwa bude shagunansu, amma kuma ta kasa hana ta’addanci da garkuwa da mutane” Injishi.

‘Yan kasuwar Dai sun yi cirko-cirko a gefe guda suna jiran abin da Allah zai yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.