Kasuwanci

Kamfanonin Indiya 135 sun zuba jarin dala biliyan 19 a Najeriya

Spread the love

Kamfanonin Indiya sama da 135 ne suka zuba jarin dala biliyan 19 a Najeriya a cikin shekaru arba’in na huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu.

Babban Kwamishinan Indiya a Najeriya, Shri Balasubramanian, ya ce sama da kamfanonin Indiya 135 sun zuba jarin dala biliyan 19 a Najeriya a cikin shekaru arba’in da suka wuce na huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu.

Mista Balasubramanian, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Abuja, ya yabawa dangantakar da ke tsakanin Indiya da Najeriya.

Ya ce dangantakar da ke tsakanin Indiya da Najeriya ta yi kyau sosai, yana mai cewa ziyarar ta zo ne domin zurfafa labarai da musanyar shirye-shiryen al’adu tsakanin kasashen biyu.

A cewarsa, ziyarar na neman inganta hanyoyin da Indiya da Najeriya za su iya yin hadin gwiwa ta hanyar musayar bayanai, da hanyoyin sadarwar labarai, da dai sauransu.

“Dangatakar al’adu, alakar da ke tsakanin mutanenmu tana da kyau kwarai da gaske, kuma da taimakon ku, tabbas zan so karfafa wannan dankon zumunci. Akwai kamfanonin Indiya sama da 135 da suka zuba jarin kusan dala biliyan 19 a Najeriya a tsawon shekaru, ba a cikin shekara daya ba, amma tsawon shekaru arba’in da suka gabata,” in ji jakadan Indiya.

Mista Balasubramanian ya kara da cewa, “Yawancinsu suna Legas, suna cikin kowane yanki na Najeriya kuma suna cikin harkar kere-kere na tattalin arziki, karafa, mai da iskar gas ko kuma magunguna. Dala biliyan uku daga cikin kayan da kamfanonin Indiya ke kerawa a Najeriya. Akwai dangantaka mai karfi da muke da ita a fannin harhada magunguna da sauran ayyukan kasuwanci.”

Babban Kwamishinan Indiya ya lura cewa Najeriya “ta kasance gida ga ‘yan Indiyawa kusan 60,000 da ke rayuwa kuma wadanda suka mayar da Najeriya gidansu a zahiri, tsawon shekaru arba’in da suka gabata.”

Mista Balasubramanian ya bayyana cewa gayyatar da Najeriya ta yi a matsayin bako mai halartar taron G20 da aka shirya gudanarwa a kasar Indiya a shekarar 2023 zai samar da wata dama ta musamman ta nuna fifikon kasashe masu tasowa ga duniya.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button