Kasuwanci

Karancin mai: NNPC, IPMAN sun kawar da fargabar ‘yan Najeriya

Spread the love

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri yayin da ake kokarin shawo kan matsalar karancin man fetur da ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar lalata wasu manyan tituna a wasu sassan jihohin arewacin kasarnan.

Shugaban kungiyar IPMAN reshen Arewacin Najeriya, Alhaji Bashir Danmalam ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Kano.

Danmalam ya bayyana cewa kimanin manyan motoci 200 dauke da kayayyaki daga Calabar jihar Cross River ana sa ran a Abuja da sauran sassan jihohin Arewa domin rabawa gidajen mai.

Shugaban na IPMAN ya ce ana sa ran motocin za su bi ta Ikom, Ogoja, Katsina Ala, Vandeikia har zuwa Lafiya zuwa Abuja.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Kamfanin Mai na Najeriya, ya ce babu bukatar tsoro da firgici, domin ana kokarin magance kalubalen karancin mai da aka samu sakamakon ambaliyar ruwa a wasu sassan jihohin Kogi da Neja wanda ya hana wucewar man fetur din da motocin dakon kaya, motoci na nan zuwa, za a rabawa Abuja da wasu jihohin arewa.

Kamfanin, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun Babban Manajan Rukunin Hulda da Jama’a na Kamfanin NNPC Ltd, Garba Muhammad, ya ce halin da ake ciki a halin yanzu layukan da ake samu a wasu sassan Abuja da kewaye ya samo asali ne sakamakon tsaikon zuwa motocin dakon mai.

Danmalam ya yabawa Manajan Daraktan Kamfanin Bututun Man Fetur da Kamfanonin Sayar da kayayyaki, Alhaji Isyaku Abdullahi bisa alkawarin tallafa wa ‘yan kasuwar da man dizal domin rage wahalhalun da suke fuskanta sakamakon tsadar kayan da ake samu.

Ya ce kamfanin mai na NNPC Limited tare da hadin gwiwar IPMAN sun yi namijin kokari wajen ganin an samar da isassun kayayyaki da kuma rabar da su inda ya ce nan ba da dadewa ba za a kawo karshen karancin man fetur.

Ya ce biyo bayan ambaliya mafi akasarin manyan titunan da ‘yan kasuwar ke amfani da su sun lalace saboda yawancin direbobin manyan motoci sun shafe kwanaki takwas zuwa tara musamman a hanyar Koton Karfe kafin su isa inda suke.

Ya lura cewa wasu daga cikin hanyoyin da abin ya shafa sun hada da titin Bida lemu-zungeru, Minna-Tagina (kilomita 6 daga Minna Makonkele) da Titin Tegina-Mokwa da kuma titin Mokwa- Makera zuwa Minna (Bakane) da Lambata-Lapai-Agaie-Bida.

Ya kuma bayyana cewa, kamfanin na NNPC ya kuma tattara jami’an hukumar kiyaye haddura ta tarayya domin su taimaka wajen share hanyoyin da abin ya shafa domin jigilar kayayyaki zuwa sassan Arewacin kasar nan.

Bugu da kari, ya ce kamfanin na NNPC ya umurci kamfanin CCC na kasar Sin da ke aiki kan hanyoyin da abin ya shafa da su koma yankunan da suka lalace domin gaggauta aikin da kuma tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa cikin sauki.

‘’Hukumar NNPC ta kuma hada Dantata & Sawoe domin fara aiki a kan lalacewar hanyoyin da abin ya shafa domin baiwa manyan motocin damar jigilar kayayyakin cikin kankanin lokaci,” in ji Danmalam.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button