Kasuwanci

Kasar Norway ta ware dala miliyan 6.3 ga manoman Najeriya a Arewa maso Gabas

Spread the love

An yi niyyar bayar da gudummawar ne don taimakawa sama da mutane 300,000 daga cikin mafiya rauni a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Gwamnatin kasar Norway ta ware dala miliyan 6.3 ga manoma a yankin arewa maso gabashin Najeriya, wani abin farin ciki da aka samu biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta janyo hasara ga manoman.

Knut Eiliv-Lein, jakadan kasar Norway a Najeriya ne ya bayyana haka a wajen bikin sanya hannu a Abuja, wanda ya nuna farkon fara aiwatar da aikin.

Aikin yana da kasafin kudi na shekaru uku na kusan dala miliyan 6.3, baya ga wasu muhimman tallafi.

An yi wannan tallafin ne tare da hadin gwiwar Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO, an yi niyya ne don taimakawa sama da mutane 300,000 daga cikin mafiya rauni a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sabbin gudummawar na zuwa ne ‘yan makonni bayan da FAO ta fitar da Binciken Abinci da Gina Jiki na Oktoba na 2022, wanda kuma aka sani da Rahoton Cadre Harmonisé, wanda ya bayyana cewa kusan mutane miliyan 17, ciki har da ‘yan gudun hijira a fadin jihohi 26 da babban birnin tarayya.

Ta yi gargadin cewa adadin ‘yan Najeriyar da ke fuskantar matsalar abinci na iya karuwa daga kimanin miliyan 17 zuwa miliyan 25.3 idan ba a yi wani abu ba don ceto matsalar abinci.

Rahoton ya bayyana tsadar kayan abinci sakamakon lalacewar gonaki da amfanin gona da shanu da kuma tsadar kayan amfanin gona a matsayin babban abin da zai iya haifar da karuwar adadin ‘yan Najeriya da matsalar abinci ta shafa a halin yanzu.

Sauran sauye-sauyen sun hada da raunin Naira, tashe-tashen hankula a Borno, Yobe, da Adamawa a arewa maso gabas, da kuma garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami a jihohin Sokoto, Kaduna, Benue da Neja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button