Kasuwanci

Kungiyar masu siyar da ‘Pure Water’ ta ƙasa ta kara farashin ruwan zuwa Naira 300 kan kowace leda

Spread the love

Kungiyar masu samar da ruwan leda (ATWAP) ta kara farashin ruwan (‘tsarkake’) zuwa Naira 300 kan kowacce jaka.

Shugabar ƙungiyar ta kasa, Clementina Ativie ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.

An cimma wannan matsaya ce baki daya a yayin taron kungiyar ATWAP na kasa a Abuja.

Ativie ya bayyana cewa karin ya samu ne sakamakon ƙarin farashin kayan da ake samu a halin yanzu da kuma yanayin tattalin arzikin Najeriya.

“Farashin ruwan leda da aka fi sani da pure water yanzu ya koma Naira 300 kan kowace jaka kamar yadda farashin kamfanin yake.

Shugabar ta kara da cewa kudin da ake kashewa ya wuce abin da za su iya dauka.

Ta ce sabon farashin zai taimaka musu wajen ci gaba da biyan kudi da ci gaba da kasuwanci.

Sanarwar ta yi kira ga ‘yan kasar da su kasance masu fahimta da hakuri da kungiyar.

ATWAP ta kara farashin jakar pure water zuwa N200 a ranar 11 ga Nuwamba, 2021.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button