Kasuwanci

Majalisar dokokin jihar Kogi ta rufe wuraren hakar ma’adinai na Dangote

Spread the love

Majalisar dokokin jihar Kogi ta umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Edward Ebuka, da ya rufe dukkan wuraren hakar ma’adanai a kananan hukumomin Ankpa da Olamaboro da kamfanin hakar ma’adinai na Dangote ke gudanarwa.

Majalisar ta kuma umurci kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) na jihar da ya tabbatar da cewa an aiwatar da wannan umarni ba tare da bata lokaci ba har sai kamfanin ya fayyace batutuwan da suka shafi ayyukansa a jihar.

Kakakin majalisar, Matthew Kolawole, ya ba da umarnin a ranar Alhamis yayin wani taron jin ra’ayin jama’a da kwamitin adhoc na majalisar ya shirya kan kudaden shiga na cikin gida na jihar Kogi.

A baya Majalisar ta gayyaci Kamfanin Siminti na Dangote, Kamfanin hakar Ma’adanai na Dangote, da Zuma Coal Mining da kuma Mogra Enerji Limited domin tattaunawa kan bukatar kamfanonin su biya ga gwamnatin jihar da kuma daukar nauyin zamantakewar kamfanoni ga al’ummomin da ke karbar bakuncin.

Kakakin majalisar wanda ya nuna rashin jin dadinsa kan ayyukan da wasu kamfanonin hakar ma’adanai ke yi a yankin gabashin jihar, ya yi nuni da cewa kamfanin hakar ma’adinai na Dangote ya gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na kwato filayen da samar da ababen more rayuwa ga al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button