Mun bawa kanana da matatsakaitan ‘yan kasuwar Najeriya tallafin N75bn saboda magance tasirin Covi-19, don haka za mu kawar da talauci a kasarnan – Gwamnatin Tarayya.

Babban Daraktan Hukumar Kananan Masana’antu (SMEDAN), Dokta Dikko Umar Radda ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ba da tallafi na Naira biliyan 75 ga masu kasuwanci a duk fadin kasar.

Dakta Radda ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Katsina yayin zantawa da manema labarai.

Ya lura cewa an bayar da kudaden ne don rage tasirin COVID-19 ga tattalin arzikin.

DG din ya kara da cewa a shekarar 2020 Gwamnatin Tarayya ta fitar da kashi 100 cikin 100 na kason kudaden su, inda ta kara da cewa “anyi hakan ne duk da kalubalen tattalin arziki”.

Don haka Dakta Radda ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda tallafawa hukumar don cimma burinta da ake fata.

Hakazalika, DG ya sake nanata kudurinsa na kawar da talauci da samar da aikin yi a duk fadin kasar.

0 thoughts on “Mun bawa kanana da matatsakaitan ‘yan kasuwar Najeriya tallafin N75bn saboda magance tasirin Covi-19, don haka za mu kawar da talauci a kasarnan – Gwamnatin Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *