Kasuwanci

Najeriya na asarar kashi 95 na danyen man da take samu daga masu wawure dukiyar kasa karkashin gwamnatin Buhari – Tony Elumelu

Spread the love

Dan kasuwan nan na Najeriya Tony Elumelu a ranar Alhamis ya bayyana cewa Najeriya na asarar kashi 95 na danyen man da take samu saboda satar barayi masu wawure dukiyar kasa karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Mista Elumelu yayin da yake mayar da martani game da ci gaban da aka samu a kasarnan, ya koka da yadda Bonny Terminal ya kamata ya rika karbar gangar danyen mai 20,000 sabanin ganga 3,000 da yake samu a kullum.

“Masu kasuwanci suna shan wahala. Ta yaya za mu yi asarar sama da kashi 95 na man da aka hako mai ta hanyar barayi? ya tambayi Mista Elumelu ta hanyar tweet. “Ku dubi tashar Bonny da ya kamata a rika karbar sama da ganga 20,000 na danyen mai a kullum, maimakon haka sai ta samu kasa da ganga 3,000, wanda hakan ya sa kamfanin @Shell ya bayyana karfin majeure.”

Kalaman nasa na zuwa ne biyo bayan rugujewar wutar lantarki da kasarnan ta fuskanta a baya-bayan nan da ke ci gaba da jefa daukacin al’ummar Najeriya cikin duhu da kuma ci gaba da tashin farashin man dizal.

Peoples Gazette a ranar Talata ta ruwaito cewa farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi a kan Naira 800 kan kowace lita, inda sabon farashin ya nuna karin farashin fanfo daga farkon N225 kan kowace lita da aka sayar a watan Janairun 2021.

Galibi dai manyan ‘yan kasuwa suna amfani da shi wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum, sakamakon rashin wutar lantarki da ake fuskanta a kasarnan, farashin man dizal, wanda ba a kayyade shi ba, ya haura sama da kashi 113 cikin 100 a cikin watanni 14 da suka wuce.

Dangane da rugujewar kasa da ta kunno kai, masu taimaka wa shugaban kasar na ci gaba da murza zarge-zarge, suna masu ikirarin cewa Najeriya ta sha fama da rugujewar wutar lantarki a lokutan gwamnatocin marigayi Umaru ‘Yar’Adua da Goodluck Jonathan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button