Kasuwanci

Najeriya za ta fara fitar da shinkafa zuwa Masar

Spread the love

Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin Tiamin Rice domin sarrafa da sayar da shinkafa a gida da waje.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Kamfanin Rice na Tiamin, Mista Aliyu Ibrahim, ya fitar a Abuja.

Aliyu ya ce an yi shirin ne da nufin noman shinkafa mai inganci da RIFAN ke yi, yayin da Tiamin ke aiwatarwa da kuma kunshin fasahar nika na zamani domin sayarwa a cikin gida da waje, musamman ga Masar.

Ya ce an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, wadda za ta fara aiki na tsawon shekaru biyu a ma’aunin tan 600 na kamfanin a kowace awa a jihar Bauchi.

“RIFAN da Tiamin suna da manufa daya a fannin noman shinkafa da nika.

“Wannan shi ne don tabbatar da dorewar tsarin sarrafa shinkafa a karkashin wani hadin gwiwa da ke neman samar da, nika da kuma kunshin shinkafar da aka sarrafa mafi inganci don fitar da kayayyaki da kasuwanci a cikin gida.

“Tare da hadakar tan 920 a cikin sa’a guda daga masana’anta guda biyu a jihohin Kano da Bauchi, Tiamin Rice na daya daga cikin manyan masu noman shinkafa a Najeriya,” in ji shi.

A cewar Aliyu, kamfanin yana kuma da gonar shinkafa hekta 10,000 a garin Udubo dake jihar Bauchi.

Ya kara da cewa kamfanin ya ci gajiyar tallafin kudi guda shida na babban bankin Najeriya.

Ya kara da cewa an dauki sama da naira biliyan 20, inda ya ce kamfanin ya samu nasarar biyan hudu daga cikin kudaden shiga tsakani.

Aliyu ya ce kamfanin Tiamin Rice shi ne kamfani na farko da ya fara samun kudaden shirin bunkasa noma na kamfanoni masu zaman kansu daga CBN.

NAN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button