Sarki Sunusi II baya cryptocurrency-Naziru Sarkin Waƙa

Sarki Sunusi II baya Cryptocurrency- Naziru Sarkin Waƙa

Mawaƙi Naziru M. Ahmad da aka fi sani da sarkin waƙa ya ce ba gaskiya bane zance da wasu ke yaɗawa cewa tsohon sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu yana yin kasuwancin cryptocurrency

Mawaƙin ya bayyana hakan ne a cikin saƙon video da ya wallafa a shafinsa na internet a ranar lahadi.

Ya ce ba gaskiya ba ne yadda wasu ke yaudarar al’umma da cewar tsohon sarkin yana yi da nufin jan hankalin mutane cikin tsarin crypto.

“Na tambaya kuma an tabbatar min da cewa ba yayi, dan haka ya kamata al’umma su faɗaka a daina yaudarar su,” a cewar sa.

Ya ce mutanen da ke cikin tsarin Cryptocurrency sun jahilci kalaman da ya yi dangane da yadda suke zuba kudi a cikin tsarin.

Ya ce waɗanda ke cikin tsarin sun jahilce shi domin ko kaɗan bai ce kada a yi cryptocurrency ba ko tsarin bai dace ba.

Ya ce ya yi mamaki yadda yaga mutane na zagi da cin mutuncinsa dangane da kalaman da ya yi.

“Ni dai na ce ba sako tsakanina da dan crypto domin kuwa shi dan crypto kana bashi kudi ya kaiwa wani zai je ya zuba su ne kawai a crypto ya ce zai samu kudi.

“Kuma idan ka aike shi ya siyo maka abu kafin yakai ya saka su, ko a bashi kudi ya biya kudi makaranta ko albashin ma’aikata maimakon ya biya su sai ya zuba su a cikin crypto,” a cewar sa.

Naziru ya ce ya sha yin aike da kudi amma sai wanda ya aika yaje ya zuba su a cikin tsarin crypto ba sau daya ko sau biyu ba.

Ya kara da cewa ko kadan bai cewa dan crypto cima zaune ba ko mai neman arziki a banza ba.

“ Kuma ni bance musu marasa wayo ba ko barayin zaune ba, haka zalika ni bance crypto baya yi ba.

Ya kuma ce akwai hanyoyin yin kasuwanci da yawa da yakamata mutane su bi don samun kudi.

“Akwai manyan ‘yan kasuwa irin su Aliko Dangote da Mustaphs AMASCO da BUA ba za su taɓa baka shawara akan crypto ba.

Sai dai su sayar da taliya da sauran su irin su Mudanseer duk ba crypto suke yi ba.

“In dai ilimin kasuwanci ne ai a gurin irin waɗan nan mutanen da na faɗa muku zamu koyi darasi domin a gurin su muka ga ta ɓulle, a cewar sa

Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *