Sunayen ƴan Arewa da suka mallaki rijiyoyin man fetur a Najeriya

Ƴan Arewa da Suka Mallaki Rijiyoyin Man Fetur
.
Jerin Sunayen Manyan hamshaƙai ƴan asalin Arewacin Najeriya da suka mallaki kamfanoni da rijiyoyin man fetir.

Kafin dai ka samu damar mallakar kamfani ko rijiyar man fetir sai hukumar dake kula da tantance samar da mai ta Najeriya wato DPR ta tantance irin mutanen da suke da sha’awar zuba Jari domin harkar Mai a ƙasar

Akwai masu kuɗi da dama da suka mallaki rijiyoyi ko filaye da kuma kamfanoni dake haƙar mai a Nageriya wato (Oil Blocks or Oil Field) kuma daga cikinsu akwai ƴan Arewa kamar haka:
.
1- Janal TY Danjuma ya Mallaki Kamfanin (SAPETRO) mai nambar rijiyar Mai OPL 246
.
2- Kanal Sani Bello Mai Kamfanin (International Petroleum Company) Mai Nambar Rijiya NOML 112 da OML 177
.
3- Alh Muhammed Ludimi Mai Nambar Rijiya OML 115
.
4- Alh Aminu Dantata Mai kamfanin (Express Petroleum Company Limited) Mai Nambar Rijiya OML 108
.
5- Alh Sela Muhammed Gombo Mai Kamfanin (Northeast Petroleum Limited) Mai nambar Rijiya OML 215
.
6- Alhaji Nasiru Ado Bayero Mai Kamfanin (Seppat Petroleum Limited) Mai Namba ASUOKPU/UMUTU
.
7- Alh Mai Daribo Mai Nambar Rijiya OML 110
.
8- Rilwan Lukman Mai kamfanin AMNI Mai Namba OML 112 da OML 117
.
9- Alh Atiku Abubakar da Ƴaar adua da kuma Bayero da suka Mallaki Kamfanin (Intels Petroleum)
.
10- Usman Dan Burran Mai Kamfanin (Oriental Energy) Mai namba OML 67
.
11- ibrahim Bunu Mai kamfanin (Optimum Petroleum) OPL 310
.
12- Alh Sale Jambo Mai Kamfanin (Northeast Petroleum) Mai Namba OPL 215
.
13- Alh Sani Bello Mai Nambar Rijiya OPL 112 DA Opl 117
.
14- Aminu Alhassan Dantata Mai Kamfanin (Express Petroleum Limited) Mai Nambar Rijiya OPL 108 DA OPL 227
.
15- Muhammed Indimi Mai kamfanin (Oriental Energy Resources) Mai Nambar rijiya OPL 115
.
16- Kase Lawan Mai kamfanin (Allied Energy Resources Big Limited) Mai Namba OPL 120 da 121
.
17- Alh Baba Lawan da Musa Ciroma da suka Mallaki Kamfanin (Sahara Energy African Oil Limited) Mai Nambar Rijiya OML 40
.
18- Alh Aliyu Abubakar Mai kamfanin (Bayelsa Oil Company Ayala) Mai Nambar Rijiya OML 46
.
Waɗannan su ne ƴan Arewa da suka Mallaki rijiyoyi da kamfanonin da ke Haƙar Nai a Najeriya
.
Yanzu haka dai ƴan asalin Najeriya su suka Mallaki kashi 52 Na Kamfanonin dake haƙar mai sai kuma Kamfanonin kasashen waje (Foreign Company) da suka Mallaki kashi 48%
.
Jahohin da ake Haƙowa Man fetir sun haɗar da Jahar Akwa Ibom da Rivers da Bayelsa sai kuma jahar Edo da Lagos da Delta da Imo sai jahar Ondo

Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *