
Idan za’a iya tunawa, tun daga ranar 19 ga Yuni, lokacin aka soma wata turka turka tsakanin fadar gamnatin Kano, Asibitin Ƙasa, da majalisar dokokin jihar Kano, inda Asibitin na ƙasa ya aika da wasiƙa ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda ya ce takardun da Muhuyi ya gabatar ga Majalisar na bogi ne, biyo bayan gayyatar da majalisar tayi masa yace wancan asibitin me ya bashi takardar.
Duk da cewa Muhuyi Magaji Rimin Gado an dakatar da Muhuyi a ranar 5 ga watan Yuli na 2021, kuma aka maye gurbinsa da Mahmoud Balarabe, da alama tsuguni bata ƙare i zuwa wannan lokacin.

Domin kuwa, idan za’a iya tunawa, kwanakin baya da suka gabata watau ranar 4-5 ga watan Oktoba na shekara 2021, Hafsat Ganduje (Gwagwgo ta amsa) , kiran hukumar EFCC.
Duk da cewar duniya a ta shaida cewar, ɗan cikin ta mai suna Abdulazeez Ganduje ne yakai ƙarar, shaidun baya-bayan nan suna so su kuma kawo tasgaro ga wannan amanna da akayi da maganar.

Majiyoyi a Fadar Gwamnatin Jihar Kano sun ce Gwamna Ganduje ya yi amannar cewa Muhuyi ne ya sa Hukumar Hukunta Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’anati, EFCC ta kama mai ɗakinsa.

Saboda haka ne yanzu zancen da akeyi, rundunar ƴan Sandan ta Jihar Kano na shirin maka tsohon Shugaban Hukumar karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado a kotu bisa zargin sa da gabatar da bayanan ƙarya ga Majalisar Dokokin Jihar Kano
Ance ɗaukar matakin nan bai rasa nasaba da yadda Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje bai ji daɗin yadda Muhuyin yayi wa Gwagwgo cinne da kuma yadda ƴan sanda suka gudanar da binciken, saboda haka ne ya dage kan cewa dole a maka Muhuyi a kotu.
A cewar majiyar mu:
“Gwamna ya ji haushin Muhuyi bisa gayyatar da EFCC ta yi wa mai ɗakinsa. Kowa ya yadda cewa Muhuyi ne ya sa a gayyace ta”, a cewar wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta.
Shin kuna ganin wannan wani salo ne na boye laifin Abdulazeez Ganduje? Ko Kuwa haƙiƙa tabbas Muhuyin ne kanwa uwar gami wajen wannan cinnen?
Bayyana ra’ayi!
Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru