Kasuwanci

Wahalar Man Fetur: ‘Yan Najeriya suna siyan litar mai tsakanin N600 zuwa N700.

Spread the love

Karancin Man Fetur a sassan kasarnan ya kara ci gaba, yayin da ‘yan Najeriya ke siyan litar mai tsakanin N600 zuwa N700.

Lamarin ya fi muni ga mazauna Abuja, babban birnin kasarnan da kuma Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya ta Najeriya ta ce a makon da ya gabata ta gano wani mai da aka gauraya da methanol, kuma ta janye man daga sassan Najeriya.

A cewar wani mai sarrafa man, an keɓe ƙayyadaddun adadin samfurin man da abin ya shafa kuma an cire shi daga kasuwa, gami da manyan motoci masu dako.

Sakamakon haka, Shugaba Muhammdu Buhari ya umurci hukumomin da suka dace da su sanya takunkumi ga duk wadanda ke da hannu wajen shigo da wannan gurbatattun mai.

Ko da yake an samu tabbacin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) na cewa lamarin zai lafa, amma babu wani abu da ke nuna hakan zai kawo karshen abin nan ba da dadewa ba.

Wannan matsala ta sa wasu matafiya, musamman ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu sun makale, inda wasu ke biyan makudan kudade sama da kashi 100 na zirga-zirgar zuwa inda suke.

Yayin da ’yan bakar kasuwar suka jeru manyan tituna suna siyar da mai da tsada ba tare da damuwa ba, direbobin motocin ‘yan kasuwa su ma sun kara kudin jigila.

A kan titin filin tashi da saukar jiragen sama na Lugbe, wasu matasa suna siyar da galan din man fetur mai lita 10 akan farashi mai tsada daga N5, 000 zuwa N7,000.

Haka kuma, an tattaro cewa wasu gidajen mai suna sayar da man tsakanin N190 zuwa N195 kowace lita.

A cikin wata hira, wani dan bakar kasuwar, Ameh, ya ce lamarin ba shi da sauƙi ga masu gudanar da bakar kasuwar da kuma da ke siya daga gidajen mai.

A cewarsa, ya sayi man ne a kan farashi mai yawa kuma ba shi da wani zabi da ya wuce ya sayar da shi kan farashin da zai iya cin riba.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa farashin litar ya tashi kwatsam daga N500 zuwa N700 a cikin sa’o’i 3 kacal, Ameh ya bayyana cewa, “da safe na sayar da mai Naira 500 a kowace lita, daga baya kuma da na je sayo wani sai gidan mai ya sayar mini kan Naira 300 kan kowace lita, sun amince za su sayar mini da galan lita 25, sai na ba su cin hancin Naira 1,500. To ka ga me ya sa muke sayarwa a kan Naira 700?

Ga mutane da yawa, abin ban takaici ne kamar yadda John Musa ya ce: “Na biya Okada N500 daga Jikwoyi zuwa Nyanya da N400 zuwa Berger. Ba ni da zabi saboda akwai mutane da yawa kuma babu abin hawa.”

Kafin karancin mai, matafiya suna biyan Naira 200 daga Jikwoyi zuwa Nyanya kan Okada yayin da ake kashe N200 don isa Berger daga Nyanya.

Wani ma’aikaci a tashar mai ta Mobil daura da Cocin Living Faith a Jikwoyi, ya ce suna jiran manyan motocin man fetur guda biyu gobe (Laraba).

Rahoton Blueprint

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button