Wasanni

Kasuwar ‘Yan kwallo: Makomar Draxler, Stones, Batshuayi, Tomori, Garcia, Brooks.

Spread the love

Leeds United na yunkurin dauko dan wasan Paris St-Germain da Jamusr Julian Draxler, mai shekara 26. (RMC Sport – in French)

Dan wasan Ingila John Stones, mai shekara 26, ya ce zai ci gaba da zama a Manchester City a wannan bazarar domin ya fafata wajen samun shiga a wurin Pep Guardiola. (Telegraph)

Dan wasan Chelsea da Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 22, ya kusa tafiya Everton domin yin zaman aro na kakar wasa daya. (ESPN)

Barcelona ta shirya tsaf domin sake yunkurin dauko dan wasan Manchester City dan kasar Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Da alama Leicester City za ta buge Manchester United a fafutukar dauko dan wasan Bournemouth da Wales David Brooks, mai shekara 23. (Manchester Evening News)

Manchester United za ta sayar da golan Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, a yayin da rahotanni ke cewa Aston Villa da Chelsea suna son dauko shi. (Express)

United na sanya ido kan halin da dan wasan Sufaniya Sergio Reguilon yake ciki a Real Madrid bayan an saki dan wasan mai shekara 23, kodayake a halin da ake ciki sun fi son dauko ‘yan wasan da ke kai hari. (ESPN)

Liverpool na duba yiwuwar sayar da dan wasan Ingila da ke buga wasa na ‘yan rukunin kasa da shekara 21 Rhian Brewster, mai shekara 20,a bazarar nan. (Sky Sports)

Paris St-Germain ta bai wa Arsenal aron golan Faransa Alphonse Areola, mai shekara 27, inda zai yi zaman kakar wasa daya. (Mirror)

Aston Villa tana son kulla yarjejeniyar gaggawa da golan Arsenal dan kasar Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 28, domin ya isa kungiyar da wuri ta yadda zai shiga wasansu na farko na kakar wasan bana ranar Lahadi. (Mail)

Daga Amir Sufi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button