Kawo karshen matsalar ta’addanci a Arewa shine babbar manufar Gwamnatin Shugaba Tinubu ~Kashim

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa kawo karshen rashin tsaro a kasar ya kasance babban ajandar gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Shettima ya yi wannan jawabi ne a wajen bude taron kwanaki biyu kan matsalar rashin tsaro a arewacin Najeriya, mai taken “Tsarin magance matsalar tsaro a Arewacin Najeriya” wanda gamayyar kungiyoyin Arewa CNG ta shirya jiya a Abuja.
Sanarwar tasa ta samu sayen Sarkin Musulmi, Mohammed Sa’ad Abubakar 111, wanda ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a iya samun nasara a yakin da ake da rashin tsaro.
Shettima, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Sanata Ibrahim Hassan, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin tarayya ba ta ja da baya wajen magance matsalar rashin tsaro a cikin al’umma ba, ya kuma yi kira da a hada kai wajen dakile wannan matsala.
Ya ce: “Na yi imanin taron da aka sanar a nan wata hanya ce ta alkawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa al’ummar kasa a jawabinsa na kaddamar da cewa kawo karshen rashin tsaro shi ne babban ajandar gwamnati.
“Don haka, ba mu raina ginshikin rawar da tsaro ke takawa a harkokin mulki ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa aka kasafta mafi girman kasafin kudin ga bangaren tsaro. Ina so in yi kira ga duk abokan tarayya da masu ruwa da tsaki da su shiga cikin wannan aikin.”
Za a iya cin nasara a yaki inji Sarkin Musulmi
A nasa jawabin, mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, wanda ya bayyana cewa za a iya samun nasara a yaki da rashin tsaro, ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su karaya, yana mai jaddada cewa dole ne al’ummar kasar su rungumi aiwatar da tsare-tsare da manufofin da ya dace.