Kawo yanzu ‘yan Nageriya suna jin da’di Kuma sun Gamsu da Gwamnatin Shugaba Tinubu ~Cewar Ministan Abuja Nyesom Wike.
Mista Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) ya ce ’yan Najeriya sun ji dadi kuma sun gamsu da abin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi.
Wike ya bayyana haka ne a yayin wani rangadin duba ayyukan gina tituna da ake gudanarwa a babban birnin kasar ranar Laraba.
A cewar Wike, saka hannun jarin da Gwamnatin FCT ta yi a kan ababen more rayuwa zai bunkasa harkokin tattalin arziki a babban birnin tarayya Abuja.
Ministan ya leka babbar hanyar wacce ta taso daga A. A Rano, bayan Villa ta Deeper Life Junction, SARS, zagayen Apo zuwa gundumar Wasa.
Kamfanin China Geo-Engineering Corporation (CGC) Nigeria Limited ne ke gina hanyar.
Wike ya kuma duba babbar hanyar N-20 ta Arewa a gundumar Jahi da kamfanin Gilmor Construction ke ginawa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne ministan ya duba hanyoyin B12, B6, da Circle Road a yankin tsakiyar Abuja
A cewarsa, hanyoyin da zarar an kammala za su bunkasa harkokin tattalin arziki a babban birnin tarayya Abuja.