Labarai

Kayiwa Allah da Annabi ka dawo Mana da SARS jihar Borno Gwamna Zullum ya faɗawa Buhari

Spread the love

Gwamnan jihar Borno Farfesa Bagana Umar Zulum (Khadimul Ummah) ya roki Maigirma shugaban ‘yan sandan Nigeria IGP Muhammad Abubakar Adamu da ya taimaka ya kawo rundinar SARS da aka rushe zuwa jihar Borno domin su taimaka wajen yaki da Boko Haram saboda amfaninsu da ya gani a zahiri

Gwamna Zulum yayi wannan rokon ne a yau Talata lokacin da Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Argebesola ya kai masa ziyara a birnin Maiduguri Zulum yace; mu a jihar Borno munga kokarin da SARS sukeyi ta hanyar amfani da karfinsu da jaruntarsu suke yakar Boko Haram da gaske

Mu ba ma goyon bayan kowani irin zalunci da wasu gurbatattun jami’an tsaro kan aikata, amma magana ta gaskiya mu anan jihar Borno kokarin da rundinar SARS suke a bangaren yaki da ta’addanci abune da ba za’a misalta ba

SARS suna yin aiki sosai wajen dawo da zaman lafiya a jihar Borno, sun maye mana gurbin kokarin da sojojin Nigeria suke yi a yaki da Boko Haram, inji Gwamna Zulum

datti datti

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button