Labarai

Kayi gaggawar komawa da tashar Jiragen Ruwa jihar Ribas Sakon ‘yan kudu ga Buhari

Spread the love

Wani jigo a jam’iyyar APC, Ibrahim Mohammed, ya roki shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta karkatar da hada-hadar jiragen ruwa daga Legas zuwa jihar Ribas saboda abubuwan dake faruwa.

Kowa dai ya ga yadda yan iska a Legas suka rika banka wa ofishohin gwamnati wuta har da ofishin hukumar kula da tashohin ruwan Najeriya dake Legas sannan sun hana a ci gaba da ayyuka kamar yadda aka saba.

Dama kuma akwai manyan tashohin ruwa jihar Ribas dake aiki yanzu haka, kawai a bunkasa su sannan a fadada na Baro dake jihar Neja sda sauran su, domin a cigaba da aiki maimakon a cigaba da amfani da na Legas.

A wasikar, Ibrahim yace yanzu abin ya kazanta, domin yan iska sun na neman karfi da yaji a samu rarrabuwar kai da tashin hankali. Abin ya kazanta saboda haka dole gwamnati ta karkata akalar zuwa wani gefen tunda wuri.

Idan ba a manta ba tun bayan fara Zanga-Zangar EndSARS, tsaro ya tabarbare a wasu jihohin kasar nan. Har zuwa safiyar Asabar din yau, yan iska na ci gaba da bankawa gidajen gwamnati wuta da kuma sace sace a jihohin Legas, Oyo, Osun, Ekiti Koros Ribas da sauran su.

A jihar Kwara ma an yi bata kashi tsakanin jami’an hukumar Kwastam da yan iska da suka dira musu. Wasu jami’ai sun samu rauni a bata kashin.(Premium times Hausa).

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button