Labarai

Kayi gaggawar sakin daliban Sheikh Dahiru Bauchi ~Kungiyar Arewa Writers ga El’rufa’i

Spread the love

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” Tana Kira Ga Gwamnatin Jihar Kaduna, Da Ta Saki Daliban Sheikh Dahiru Usman Bauchi Da Ta Tsare Na Tsawon Kwanaki Biyu A Hannunta

Daga Ƙungiyar Arewa Media Writers

A ranar Laraba da ta gabata 13/01/2021 da misalin karfe 12:00 na dare, gamayyar jami’an tsaron jihar Kaduna, suka je mazaunin wasu daga cikin ɗaliban Shahararren Malamin Addinin Musulunci kuma babban Jagoran Ɗarikar Tijjaniya a Nijeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, su kayi Awon gaba da ɗaliban da ba’asan adadin su ba, bayan sun harba musu borkonon tsohuwa.

Gwamnatin Jihar Kaduna tace; ta kama ɗaliban ne kan zargin sun karya dokar da gwamnatin jihar ta saka wajan yaƙi da cutar Corona.

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ta tuntubi ɗaya daga cikin malaman da suke kula da ɗaliban da aka kama inda ya bayyanawa kungiyar cewa; “Su basu san wacce doka suka karya ba, har ya sanya a kazo aka kama musu ɗalibai ba, domin sun jima da sallamar ɗalibai zuwa gidadajen iyayan su tun biyo bayan zartas da wannan doka da Gwamnatin Jihar tayi, sai dai sauran mutane da wannan gida ya zame musu mazauni, idan sukanje kasuwa suka taso sukan zo su kwana anan wajen, domin nan ne makwancin su kuma wasun su duk suna da iyalai”.

Babu shakka wannan samame da Gwamnatin jihar Kaduna ta kai ga Almajiran Shehun Malamin yabar baya da kura, domin tuni kafafen sadarwar zamani suka zafafa da muhawarori tare da kiraye-kiraye ga gwamnatin Jihar da ta gaggauta sakin wadannan mutane da ta kama.

Ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, take kira ga gwamnatin jihar Kaduna da tayi ƙoƙarin sulhuntawa dasu akan ƙoƙarin da gwamnatin jihar take yi, wajan yaƙi da cutar Corona, tare da sakinsu domin su koma cikin ‘yan uwansu da kuma iyalansu.

Kungiyar “Arewa Media Writers” tana fatan gwamnatin jihar za ta ƙarɓi koken ta, domin ɗaliban su samu damar sararawa bayan sun shafe tsawon kwanaki biyu suna garƙame a hannun gwamnatin.

Haka zalika ƙungiyar tana addu’ar Allah ya kawo mana ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankinmu na Arewa. Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button