Kefas Agbu na PDP ya zama zababben gwamnan Taraba
Jami’in kula da masu kada kuri’a na jihar Farfesa M.A. Abdulazeez ya bayyana Agbu a matsayin wanda ya lashe zaben da karfe 12:30 na safiyar ranar Talata.
.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Kefas Agbu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Taraba.
Agbu, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya samu kuri’u 257,926 inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Muhammad Yahaya, wanda ya samu kuri’u 202,277.
A matsayi na uku, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Emmanuel Bwacha, ya samu kuri’u 142,502.
Jami’in kula da masu kada kuri’a na jihar Farfesa M.A. Abdulazeez ya bayyana Agbu a matsayin wanda ya lashe zaben da misalin karfe 12:30 na safiyar ranar Talata, bayan samun nasarar da ya samu a matsayin wanda ya cika sharuddan nadin nasa zababben gwamnan jihar.
Abdulazeez ya yi kira ga dukkan wadanda suka fafata da su “yi hakuri da juna” ya kara da cewa, “Muna yin haka ne domin tabbatar da cewa dimokuradiyya ta yi nisa a Najeriya.