Kima da Darajar Gwamnatin Jihar kano zai zube a idon duniya idan ta janye mukabalar ~Inji Shekh Abdujabbar Nasiru kabara
A wani sako daga shafi Makarantar Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara Ashabul kahfi warraqeem ya nuna Jan Hankalin Gwamnatin jihar Kano tare da nuna Mata Matsayin mukabala ga dai Sakon kamar Haka….
Ga wani muhimmiyar saqo!
GODIYA TARE DA TINI GA GWAMNATIN JIHAR KANO
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wabarakatuhu!
Da Yawun Dukkan Al’ummar Musulmi Na Wannan Jiha Mai Albarka Waɗanda Addinin Su Ya Dame Su, Waɗanda Suke Cikin Matukar Damuwa Bisa Wannan Yanayi Na Rashin Tabbaci Akan Haƙikar Addinin Asali Da Annabin Mu Muhammad (S.a.w.w) Ya Barwa Al’ummar Sa Mu ke Gabatar Da Wannan Kira Da Babbar Murya Izuwa Ga Gwamnatin Jihar Kano Ƙarƙashin Jagorancin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Kamar Haka:-
Godiya Ta Musamman Gare Shi Bisa Amincewar Sa Da Gabatar da MUƘABALA
Ta Ilmi Zalla Cikin Lumana Da Mutunci Da Girmama Juna Tsakanin Ɓangarorin Malamai Guda Biyu
A- Masu Ganin Cewa Akwai Matsala A cikin Hadisan Da Suke Cikin Litattafan Muslunci Wanda Suka Haɗar da Cin Mutuncin Ma’aikin Allah (S.a.w.w) Da Sauya Masa Wasu Abubuwa A Cikin Addinin Da Ya zo Da Shi Na Gaskiya Wanda Yake Wakilta Wannan
Ɓangaren Shi ne:-
Shaikh ABDULJABBAR KABARA
B- Masu Ganin Cewa Waɗannan Al’amura Ba Haka Suke Ba Dukkan Abin Da Suke Cikin Waɗannan Litattafai (BUKHARI DA MUSULM)
Sun Inganta Kuma Babu Cin Mutuncin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam A Cikin Su Waɗanda Su ke Wakiltar Wannan Ɓangare Su ne Kamar Haka:-
1- Malam Ƙaribu Kabara ( Ƙadiriyyah )
2- Mallam Shehi Shehi Mai Hula ( Tijjaniyyah )
3- Malam Bashir Tijjani Ƴan Mota
( Tijjaniyyah )
4- Malam Nasir Adam
( Tijjaniyyah )
5- Malam Umar Sani Fagge
6- Malam Ibrahim Khalil
7- Mallam Bashir Ali Umar ( Izalah )
8- Malam Sani R/ Lemo ( Izalah )
9- Malam Abdallah Saleh Pakistan ( Izalah )
10- Malam Abdulwahab Abdallah ( Izalah )
11- Malam Sanusi Lamiɗo Sanusi (TSIGAGGEN SARKIN KANO)
Lallai Hukuma Ta Sani Yin Wannan Zama Waɗannan Ɓangarori Shi ne Mas’laha
Shi ne Hanyar Samar da Haɗin Kai Tsakanin Al’umma Da Tsare Imanin Mutane Daga Tababar Da Suke Ciki A Halin Yanzu
Rashin Yin Wannan Zama Zai Haifar Da Saɓanin Waɗancen Natijoji Da Mu ka Ambata A Sama Tare Da Raguwar Ƙimar Hukuma Bisa Rashin Cika Alƙawari.
Allah Ka Bayyana Mana Gaskiya Ka Ba Mu Ikon Bin ta
Ka Bayyana Mana Ƙarya Ka Ba Mu Ikon Guje Mata Aameen.
Wassalaamu Alaikum Wa Rahmatullah.
20/02/2021