Lafiya

Kimanin Mutanen 400 Sun Kamu Da Cutar Corona Virus A Gidajen Yari A Kasar Morocco.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Jami’an gwamnatin kasar Morocco sun bayyana cewa fursinoni da ma’aikatan gidajen yari a kasar kimanin 400 ne suka kamu da cutar Corona.

Kamfanin dillancin labaran Anatoly ya nakalto hukumar gidajen yarin ta kasar ta na yin wannan bayani a yau Lahadi.

Ta kuma kara da cewa fursinoni da ma’aikatan gidajen yari 397 ne suka kamu da cutar a gidajen yarin kasar, sannan 301 daga cikinsu fursinoni ne a yayin da 96 kuma ma’aikatan gidajen yarin. Labarin ya kara da cewa mutane 244 daga cikinsu sun warke daga cutar.

Kasar Morocco dai tana da fursinoni kimani 80,000 a gidajen yarin kasar, sannan tana da ma’aikatan gidajen yari 10,200.

Mutane 5,910 ne suka kamu da cutar Corona a kasar Morocco ya zuwa yanzu, 186 daga cikinsu sun rasa rayukansu sanadiyyar cutar, a yayin da mutane 2,461 kuma suka warke daga cutar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button