Ilimi

Kimanin Yara Miliyan 46 Yan Najeriya Ba Sa Zuwa Makaranta A Cewar Hukumar NITDA

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani ta Najeriya (NITDA), ta bayyana adadin Yara Miliyan 46 ne basa zuwa Makaranta sakamakon barkewar cutar coronavirus a Najeriya.

Babban darektan hukumar NITDA, Kashifu Inuwa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya.

Haka zalika ya bayyana cewa A kalla a kwai Dalubai kimanin 24,372 da suka samu horo a karkashin Manhajar da hukumar ta samar dan tallafawa Dalubai a lokacin da suke zaman gida sakamakon cutar Covid-19.

Wadanda Suka halarci taron Sun hada Da Ministan Sadarwa Dakat Isa Ali Pantami tare da Sakataran hukumar hadi da Ministan Ilimi, tare da sauran mambobi dake Ma’aikatu biyun.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button