
Daga Comr Yaseer Alhassan
Tsohuwar ministar Mai, Diezani Alison Maduekwe ta bayyana cewa abin takaicine yanda tarbiya ke tabarbarewa tsakanin matasa.
Tace yanzu ‘yan Damfara yanar gizo da ake kira da Yahoo-Yahoo sune suka zama abin koyin matasan a Najeriya.
Tace amma fa matasan su sani cewa babu wata hanyar kaiwa ga nasara a Rayuwa ba tare da aiki tukuru da jajircewa ba.
Ta bayyana hakane a wata ganawa da aka yi da ita kan al’ummar kabilar Ijaw wanda shima tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya halarta.