Cibiyar bunkasa fasaha ta Dagona Science and Technical ta kirkiri wani jirgin leken asiri wanda yake aikewa da bayanai kaitsaye ta bidiyo Kaitsaye.

Shugaban cibiyar bunkasa fasha ta Dagona Science and technical Usman Umar Dagona ya ce, bayan ya dauki wasu matakai yayin gina jirgin mai suna Mini Spying Drone, ba dukkan jirage marasa matuka bane suke da inganci iri daya da siffofin Spying Drone ba, yanayin rashin ganowa yasa hakan ya zama abin ban mamaki tsakanin wasu.

Jirgin dan karami ne, an sanya kyamara mai saurin 3D a kansa, kuma a halin yanzu yana aiko masa da saƙo kaitsaye daga inda yake.

Matashi Usman Umar Dagona dai shine wanda yazo na daya a gasar Chemistry ta kasa a shekarar 2020, haka kuma shine yazo na biyu a gasar Chemistry ta Duniya duka dai a shekarar 2020.

Yanzu dai matashin wanda yake dan asalin yankin Arewa maso Gabas ne ya mayar da hankali wajen kere-kere na fasaha, musamman ma wadanda suke taimakawa wajen samar da tsaro kasa.

Ko a kwanakin baya ma sai da Matashin ya kirkiri wata motar leken asiri wadda take da gudun tsiya, haka kuma itama ta kasance tana turawa da bayanai kaitsaye.

Ga dai bidiyon jirgin mai suna Mini Spying Drone.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *