Mohammed Bazoum ya isa kasar Jamhuriyar Congo Brazzaville cikin yanayi na ruwan sama, domin kaddamar da Denis Sassou Nguesso.

Shugaban kasar Jamhuriyar, Nijar, Mista Mohamed Bazoum yammacin nan ne ya isa kasar Jamhuriyar Congo Brazzaville cikin yanayi na ruwan sama mai karfin gaske, inda zai halarci bikin saka jari da aiwatar da kaddamar da Denis Sassou Nguesso, wanda aka sake zaba a shugabancin kasarsa wani sabon wa’adi.

Wannan bikin zai gudana ne a wannan Juma’ar, 16 ga Afrilu, 2021, a gaban Shugabannin kasashe da dama.

Rahoto
Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *