Kimiya Da Fasaha

Kimiyya Da Fasaha: Inksnatio A Zahirinta DAma Kuma Fasaharta (Kashi Na Daya).

Spread the love

Na tabbata mai karatu zaiso yasan yaya asalin abin da kuma yadda yake a fasahance da tsarinta na asali ta yadda take tafiya.

Wannan rubutu na shirya yinshi ne bayan da naci karo da rubutun shahararren marubuci a Arewa wato Datti Assalafiy, duk cewa shi kansa yayi duba ga
abin ta fuskar addini amma yana da kyau ya dubeta ta fuskar fasaha kafin yayi rubutun, dan haka duk wanda zai iya sharing yaturamar wannan rubutun insha Allahu shi kansa zai karu.

Menene Inksnation?
Kamar yadda wadanda suka kawo ta sukayi ikrari Inksnation fasaha ce da ta biyo hanyar fasahar kudin lantarki da ake kiranta Cryptocurrency, kamar yadda suka ruwaito an fito da ita ne domin rage wa mutane talauci da kuma basu tallafi na musamman ganin yadda duniyar mu yanzu take fama da subucewar ayyuka a hannun mutane, Kamar yadda akai hasashe masana sukace nan da kamar shekarar 2025 miliyoyin mutane zasu rasa ayyukansu wanda wadannan ayyukan duka za’a maye gurbinsu da “Sakago” wato (Robot a turance). Wannan yasa Inksnation sukayi kokarin kawo wannan tsarin kamar yadda suka fada domin suraba mutane da wahalhalu da zasu iya shiga nan gaba sakamakon rashin aikin yi.

Ita dai Inksnation na dauke tsarukan daban daban har wajen tsaruka guda hudu, sune kamar haka, BRONZE, SILVER, GOLD, DIAMOND. A duka wadannan tsarukan kowane tsari yafi dan uwansa romo da abinda ake samu. Domin yin register kuwa ana biyan daga abinda yakai 1000 zuwa sama, ma’ana domin kazama member din daya daga cikin tsarukan kuma zasu biya mutane ne kowane wata ta hanyar abinda suka kira da “PinKoin”.
Kamar dai yadda suka fada wannan Pinkoin din shine zaka canza shi yazama farin kudi a account dinka, kuma duk wanda yayi register dasu zai iya samun abin da yakai sama da 200,000.

Inda gizo ke sakar shin Inksnation Gaskiya ne? Babu yaudara cikin ta ba kuma ‘Yan damfara bane?

Magana ta Gaskiya a fasahance inksnation bata cika ka’idojin wannan hanyar kasuwanci da kuma fasahar Cryptocurrency ba sam sam. Ga dukkan wani kamfani da take shirin shiga wannan harkar dole ta gabatarwa da duniya abinda ake kira “Whitepaper”, Whitepaper takarda ce ko kuma ince hanya ce da dukkan kamfanonuwa da suke kasuwanci da kuma harkar Crytocurrency suke bayani dalla dallah game da fasaha da hanyoyin tabbatar da tsaron dukiyar al’umma da dabarun kasuwanci da sukeyi ko kuma zasuyi ga masu zuba jari ko kuma masana.

Magana ta gaskiya a duk binkicena da nayi har yanzu banyi karo da Whitepapern Inksnation ba, kuma hatta a shafinsu na Inksnation.io Button link dinda ke nuna alamar in kadanna shi zaka sauke Whitepapernsu baya aiki. Haka Inksnation tayi magana akan cewa tana da Node dinta (Ma’ana nodes dinda zasuyi yawo akan Fasahar BlockChain) nuna hakan tamkar nuni da cewa ta kirkiri nata fasahar ne dai dai na fasahar da ake kira BlockChain.

Duk da babu mai in kari amma kuma ta kasa gabatar Whitepaper na wannan Nodes dinda take kira da InksNode. A rubutu na gaba zan fadada game da abinda ake nufi da BlockChain da kuma aikinta a fasahar Crytocurrency.
.
Inksnation tana karban 1000 a hannun duk mai register da ita, ma’ana dole kabiya daga abinda yakama 1000 zuwa sama yadanganci tsarin da kazaba ne a yayin register. Sabanin dukkan kamfanonin Crytocurrency ne wannan domin kuwa kowane cryptocurrency da aka kawo kamar daga Bitcoin, BitcoinCash, Electorenum, Ethereum da Sauransu babu wanda yataba tambayar kudi a hannun mutane hasalima dukkan wani sabbin fitowar wadannan kudade kyauta suke baiwa mutane ICO dinsu (Initial Coin Offering), ta hanyar abinda ake kira “Airdrop”. Ma’ana zakayi register da sune sannan subaka link da zaka gayyato musu mutane sai su biyaka ladan aikin ka. Meyasa inksnation zata karbi kudin mutane? Anya babu lauje cikin nadi kuwa?
.
Inksnation bata da takamaimai Exchange market
Kasacenwar Crytocurrency ba kudi bane na zahiri dole kana bukatar kasuwar zakaje kacanzata domin ya zame ma kudin zahiri da zakayi amfani dashi walau kasiyar ko kuma kucanza da wani.

A zance na zahiri har maganar da nake banga kasuwa daya na cryptocurrency da Inksnation ya fito da ita matsayin nanne inda mutane zasu canza kudin dan yazame musu mai amfani ba. Dan haka ga duk wanda yakeso yashiga yana da kyau ya nazarci wadanna abubuwa da na lissafo dan gudun wani abun.

Zan dakata anan Insha ALLAHU rubutu na gaba zan fadada Bayani game da fasahohin Cryptocurrency da BlockChain da kuma yanayin Bitcoin.
22/07/2020
Muhammad Baba Goni (Royalmaster)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button