Kin bayyana kadarorinsa da zargin rashawa kotun da’ar Ma’aikata ta gayyaci magu
Hukumar da’ar ma’aikata ta gayyaci dakataccen shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati, Ibrahim Magu, don amsa tambayoyi kan zargin cin hanci da rashawa da ya shafi karya ka’idojin
wani rahoto na Peoples Gazette ya ce. A cikin wata Nuwamba 2, 2020, wasikar da jaridar ta samu, an nemi Magu da ya kawo takardun dukkan bayanan kadarorinsa tun daga lokacin da ya shiga aikin gwamnati. Kwafin wasikun nadin mukamai da kuma bayanan aiki daga watan Janairu zuwa Mayu 2020 na daga cikin takardun da aka nemi Magu ya kawo, da kuma duk wasu takardu na mallakar filaye da suaransu
Gayyatar ta zo ne watanni bayan dakatar da Magu daga mukaminsa bisa zargin rashawa.
An zarge shi da sayen wani gida a Dubai na sama da N570m kuma ba zai iya lissafin kudin da ya karba sama da N500bn da EFCC ta kwato ba amma ya musanta zargin.
Kwamitin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa karkashin jagorancin Mai Shari’a Ayo Salami (mai ritaya), ya kasa tabbatar da karar da ya shigar a kan Magu, maimakon haka sai ya koma amfani da hanyoyi daban-daban a kokarin da yake na neman wata hanya..