Kinnafas kuskure yasa ya Shiga motar haya mallakin wani direba daya sace kwanakin baya..
A cewar rahotanni, an yi garkuwa da wanda da wani, direba, a kan hanyar Kankara a cikin jihar Katsina yayin dawowa daga Kano kimanin watanni biyu da suka gabata.
An bayar da rahoton cewa ya kwashe makonni uku a tsare sannan aka sake shi bayan ya biya kudin da ba a bayyana yawansu ba a matsayin fansa.
Rahotan da muke samu ya ruwaito wani dan kungiyar kwadagon zirga zirgar motoci (NURTW) ya ce, wanda ake zargin ya gane shi ne lokacin da ya hau motarsa a kan hanyarsa ta zuwa jihar Kano.
“Direban ya yi saurin gano shi saboda lamarin ya faru ba da dadewa ba,” in ji jami’in na NURTW.
“Bayan gano shi, sai ya sanar da shugabannin su wadanda su kuma suka sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa.”
Rahotanni sun ce shugabannin NURTW sun nemi direban ya matsa zuwa tashar motar Kwannawa da ke karamar hukumar Dange-Shuni na jihar, inda ’yan sanda suka tare motar.
‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargin tare da tura shi ofishinsu.
Yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi dan kungiyar masu garkuwa da mutane ne.
Tuni aka mayar da shi hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar don gudanar da bincike.