Labarai
Kisan manoma a Borno Shugaba Buhari Yace mahaukata ne masu kisan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa kan kisan manoma a gonakin shinkafa a Zabarmari, a karamar hukumar Jere ta jihar Borno.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, Mista Buhari ya bayyana kashe-kashen ‘yan ta’addan a matsayin hauka.
“Ina Allah wadai da kisan da‘ yan ta’adda suka yi wa manomanmu masu kwazo a jihar Borno.
“Duk kasar nan ta yi rauni da wadannan kashe-kashen rashin hankali. Tunanina yana tare da danginsu a wannan lokacin na baƙin ciki. Allah Ka sa rayukansu su Huta Cikin salama
Mista Buhari ya ce gwamnatin ta bayarda dukkan goyon bayan da ake bukata ga sojojin “don daukar duk matakan da suka dace don kare mutanen kasar da yankinta.”