Siyasa

Ko A Baiwa Inyamuri Shugabancin Najeriya Ko Kuma Ta Watse A 2023, Inji Tsohon Shugaban PDP Nwodo.

Spread the love

Tsohon gwamnan Enugu kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Okwesilieze Nwodo ya bayyana cewa a shekarar 2023 Inyamurine zai zama shugaban kasar Najeriya indai ana so kasar ta dore a matsayin dunkulalliyar kasa.

Ya bayyana hakane yayin da ya cika shekaru 70 a wata hira da yayi da Sunnews, kamar yanda hutudole ya samo muku. Ya bayyana cewa babban darasin da ya koya a Rayuwa shine duk wata matsala akwai maganinta, kawai mutum na bukatar nutsuwa ne da kuma jajircewa, yayi gargadi kan nasarar rana daya ko kuma bin hanyar da ba daidai ba akai ga nasara wanda yace hakan zai karene da dana sani.

Nwodo ya bayyana cewa, Maganar PDP ko ma kowace jam’iyya ta sake baiwa dan Arewa ko kuma ace koma daga inane shugaban kasar da ya cancanta ya fito su basu yadda ba. Mun ruwaito muku Nwodo na cewa, duka manyan kabilun kasarnan sun yi mulki in banda Inyamurai.

Yace an baiwa yarbawa mulki dan su huce haushin zaben abiola dan haka suma a basu mulki dan su huce haushin yakin basasa da aka yi shekaru 50 da suka gabata. Ya kuma ce tun bayan yakin har zuwa yanzu ana nuna musu wariya.

Da aka tambayeshi yana ganin Inyamuri zai iya zama shugaban kasa nan gaba kuwa, sai yace ai idan Inyamuri bai zama shugaban kasa a shekarar 2023 ba to Najeriya zata watsene, lura da yanda su Inyamurai aka samu kungiyoyi da dama suke kiran a basu kasarsu ta Biafra, Yarbawa ma zasu fara kiran a basu kasar Oduduwa sannan suma yankin Tsakiyar Najeriya zasu balle.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button